Pars Today
Gwamnatin Birma ko Myammar ta ce za ta bude sansanin don karbar 'yan gudun hijira Rohingya dake kaurewa hare haren da ake kai masu a kasar.
Majalisar Dinkin Duniya ta fitar da wasu alkalumma dake cewa yawan musulmi 'yan Rohingya da suka rasa rayukansu a hare-haren da sojojin kasar Myanmar suke kai masu ya haura dubu guda.
Kungiyar Hizbullah a kasar Lebanon ta yi tir da Allah wadai da harin ta’addancin da aka kai birnin Barcelona na kasar Spain, tare da bayyana hakan a matsayin hankoron bata sunan addinin muslunci.
Wakilan kasashen musulmi 57 na kungiyar OIC da suka taru yau a birnin Satambul na Turkiyya sunyi tir da abunda suka kira tsokana na yahudawan mamaya na Isra'ila a masallacin Al'Aqsa dake birnin Qudus.
Tsohon muftin kasar masar kuma babban malami addini a kasar ya yi kira ga musulmi su yi hattara da bin tsarin karantarwa na kasashen yamma wanda aka gina kan kiyayya ga addinin musulunci.
Bayan shafe kwanaki 15 na kaucewa sallah a cikin masallacin Kudus, ana sa ran Palasdinawa zasu gudanar da Sallar Juma'a a harabar masallacin.
A kallah Palasdinawa hudu ne suka yi shahada a yayin da jami'an tsaro yahudawan mamaya na Isra'ila suka farma masu bayan sallah Juma'a a jiya.
Wasu jagororin al'ummar musulmin turai sun hallara a wani gangami na kyammar ayyukan ta'addanci a birnin Balin na Jamus domin nunawa duniya yadda addinin na Islama ba shi da wata alaka da ta'addaci.
Majalisar musulmin kasar Birtaniya ta fitar da wani bayani, wanda a cikinsa ta nuna damuwa kan karuwar ayyukan nuna kyama ga musulmi a fadin kasar.
A yau ake raya edul-ghadir a duniyar musulmi