Sep 09, 2017 08:50 UTC
  • Gwamnatin Myammar Za Ta Budewa Musulmin Rohingya Sansanoni

Gwamnatin Birma ko Myammar ta ce za ta bude sansanin don karbar 'yan gudun hijira Rohingya dake kaurewa hare haren da ake kai masu a kasar.

Mujallar Global New Light mallakin gwamnatin Myammar din ta ce za'a bude sansanonin ne a arewaci da kudanci da kuma tsakiyar kasar domin karbar musulmin na Rohingya don kawo musu dauki da kuma kula da kiwan lafiyarsu.

Wannan dai shi ne bayyani irinsa na farko da gwamanatin Myammar ta yi tun soma kisan kiyashin da akewa musulmin na Rohingya a tsawan kwanaki 15.

A baya baya nan dai shugabar gwamnatin Myammar din Aung San Suu Kyi, ta sha shan suka daga kungiyoyi da kasasshen duniya kan rashin daukar mataki ko tsawatawa dangane da kisan kiyashin da akewa musulmin 'yan kabilar Rohingya.

Tags