Dec 20, 2016 12:43 UTC
  • An Samu Karuwar Ayyukan Kin Jinin Musulmi A Birtaniya

Majalisar musulmin kasar Birtaniya ta fitar da wani bayani, wanda a cikinsa ta nuna damuwa kan karuwar ayyukan nuna kyama ga musulmi a fadin kasar.

A zaman da majalisar ta gudanar a jiya a birnin Londan, ta fitar da bayani da ke kiran mahukunta  akasar ta Birtaniya, da su dauki matakan kare rayukan musulmi da dukiyoyinsu da kuma mutuncinsu a kasar.

Wannan kira ya zo ne sakamakon abubuwan da suke wakana a halin yanzu a wasu birane na kasar ta Birtaniya, inda aka samu wasu kungiyoyin masu kymaar musulmi da suke kai hare-hare kan cibiyoyin musulmi da masallatai, da hakan ya hada har da wasu birane da ke cikin yankin Scotland.

A kwanakin baya ma wata kotun birnin Londan ta daure wasu 'yan kasar ta Birtaniya da suka keta alfarmar wani masallaci a birnin.

Musulmin Birtaniya dai sun bayyana karuwar ayyukan nuna kyama a gare su ne a cikin lokutan baya-bayan nan, tun bayan cin zarafin wasu musulmin da aka yi a birnin Manchester a cikin shekara ta 2015 da ta gabata.

Tags