Jul 22, 2017 05:32 UTC
  • Yadda HKI Ke Ci Gaba Da Azabtawa Palasdinawa

A kallah Palasdinawa hudu ne suka yi shahada a yayin da jami'an tsaro yahudawan mamaya na Isra'ila suka farma masu bayan sallah Juma'a a jiya.

Ko baya ga wadanda sukayi shahada da akwai daririwan Palasdinawa da suka jikkata a lokacin da jmai'an tsaro Is'ralar suka yi amfani da hayaki mai sa hawaye da kuma karfin tsiya don tarwatsa Palasdinawan dake sallar Juma'a a cikin titunan dake kewaye da masallacin Al'Aqsa dake birnin Qudus.

Wannan daiya biyo bayan da a waccen juma'ar data gabata mahukunatn yahudawan suka hana sallar Juma'a.

Palasdinawa dai sun bijirewa sabbin matakan da mahukuntan yahudawan suka dauka domin hana wani rukuni na jama’a zuwa kusa da masallacin.

Sabbin matakan sun hada da cewa 'yan sama da shekara 50 ne kawai za'a baiwa damar shiga masallacin da kuma yin amfani da na'urar caje mutane kafin shiga masallacin. 

Domin kalubalantar wadanan matakan ne Palasdinawa suka dau matakin yin sallah a wajen masallacin maimakon cikinsa.

Dama kafin hakan an share tsawon kwanaki ana zaman dar dar, sakamakon matakin rufe masallacin da mahukuntan yahudawan suka dauka.

Kasashen duniya da dama ne suka yi suka dangane da wannan mataki, wanda ya haifar da bore musamman daga bangaren Falasdinawa.

Ministocin harkokin wajen kasashen Jodan da kuma Hadaddiyar daular Larabawa sun bukaci bude masallacin ga masu ibada ba tare da wata wata ba, tare da kuam da kira ga kasashen duniya dasu shiga lamarin.

Shi ma dai a nasa bangare shugaban kungiyar kasashen larabawa, Abul Gheit, ya yi Allah wadai da amfani da karfi da kuma harsashen bindiga na yahudawan Isra'ila akan fararen hula.

Wata sanarwa da kakakinsa ya fitar ta ja kunnan Isra'ila akan fuskantar babban fishin Palasdinawa, da Larabawa da kuma musulmin duniya akan wadanan matakan data dauka a baya bayan nan.  

Shi dai firaministan Isra'ila Benjaminin Netanyahu ya nace kan cewa ba zai yiwa matakan dake baiwa masu ibada musulmin da yahudawan ziyartar masallacin ba a ko da yaushe. 

A halinda ake ciki dai shugaban Palasdinawa Mahmud Abass ya sanar a jiya Juma'a da katse du wata tuntuba da mahukuntan yahudawan mamayar har sai Is'ra'ilar ta janye shigayen binciken data kafa a shigar masallacin na Al'Aqsa dake zamen wuri na uku mafi tsarki na al'ummar musulmi.

 

Tags