-
Sojojin Nijeriya Sun Sami Gagarumar Nasara A Kan 'Yan Boko Haram
Apr 17, 2016 23:31A ci gaba da kokarin da sojojin Nijeriya suke yi na kawo karshen kungiyar nan ta Boko Haram, sojojin sun sanar da wata gagarumar nasarar da suka samu a kan 'yan kungiyar biyo bayan wani hari da suka kai daya daga cikin maboyan 'yan kungiyar.
-
Shekaru Biyu Da Sace ‘Yan Matan Chibok
Apr 14, 2016 06:33Yau shekaru biyu ke nan cur da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace daliban ‘yan matan sakadaren a garin Chibok a jihar Borno.
-
Buhari Ya Sha Alwashin Daukar Tsauraran Matakai Kan Masu Fasa Bututun Mai Na Niger-Delta
Apr 14, 2016 00:13Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya sha alwashin daukan tsauraran matakan ba sani ba sabo kan mutanen da suke hannu cikin hare-haren baya-bayan nan kan batutun man fetur da iskar gas na a yankin Niger-Delta mai arzikin man fetur.
-
Wasu Iyayen 'Yan Matan Chibok Sun Gano 'Ya'yansu Cikin Faifan Bidiyon Boko Haram
Apr 13, 2016 23:24Wasu iyayen 'yan matan makarantar sakandaren nan ta Chibok da ke jihar Bornon Nijeriya sun bayyana cewar sun gano 'ya'yansu da kungiyar Boko Haram ta sace shekaru biyu da suka gabata cikin wani sabon faifan bidiyo da kungiyar ta fitar a shekaran jiya Talata.
-
Hira Da Daraktan Amnesty Int. A Najeriya Kan Kisan Gillar Zaria
Apr 13, 2016 10:09Babban daraktan kungiyar Amnesty Int. a reashenta na Najeriya Muhammad Kawu Ibrahim ya zanta da Sashen Hausa na Pars Today Tehran, kan kisan gillar da aka yi wa mabiya mazhabar shi'a a Zaria.
-
MDD Ta Jaddada Tsananin Damuwarta Kan Makomar 'Yan Matan Chibok Da Aka Sace
Apr 13, 2016 06:46Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada tsananin damuwarta kan makomar 'yan matan makarantar sakandare na garin Chibok da mayakan kungiyar Boko Haram suka sace a jihar Bornon Nigeriya yau tsawon shekaru kimanin biyu da suka gabata.
-
Amnesty Int. Ta Bukaci Sojoji Su Yi Bayani Kan Kisan Gilla A Zaria
Apr 13, 2016 00:07Kungiyar kare hakkin bil adama ta kasa da kasa Amnesty International ta bukaci sojojin Najeriya su yi bayani kan kisan gillar da aka yi a Zaria a kan mabiya mazhabar shi'a.
-
Ganawar Shugaba Buhari Na Najeriya Da XI Jinping Na China
Apr 12, 2016 23:36Shugabannin kasashen Najeriya da na China sun gana a jiya a birnin Beijin, inda suka tattauna muhimman batutuwa da suka shafi alaka tsakanin kasashen biyu.
-
Najeriya: Matasa Sun Bukaci Shugaba Buhari Da Ya Cika Alkawali
Apr 07, 2016 10:50Daruruwan matasa daga sassa na Najeriya sun gudanar da gangami da jerin gwani a Abuja, suna kira shugaba Buhari da ya ci alkawullansa, domin sun zabe shi ne saboda amincewar da suka yi da shi.
-
Za A Rage Shigo Da Abinci Domin Inganta Noma A Najeriya
Apr 07, 2016 10:34Shugabab Buhari na Najeriya ya sheda cewa za a rage shigo da abinci domin inda ayyukan noman a bincin a cikin gida.