Najeriya: Matasa Sun Bukaci Shugaba Buhari Da Ya Cika Alkawali
Apr 07, 2016 15:20 UTC
Daruruwan matasa daga sassa na Najeriya sun gudanar da gangami da jerin gwani a Abuja, suna kira shugaba Buhari da ya ci alkawullansa, domin sun zabe shi ne saboda amincewar da suka yi da shi.
Daruruwan matasa daga sassa na Najeriya sun gudanar da gangami da jerin gwani a Abuja, suna kira shugaba Buhari da ya ci alkawullansa, domin sun zabe shi ne saboda amincewar da suka yi da shi, kuma a cewarsu wasu na hannun damarsa ne ke hana ruwa gudu, wadanda ya kamata ya yi watsi da su.
Muhammad Sani Abubakar ya halarci wurin, ga abin da wasu daga cikinsu suke sheda masa.
Tags