Shekaru Biyu Da Sace ‘Yan Matan Chibok
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i3874-shekaru_biyu_da_sace_yan_matan_chibok
Yau shekaru biyu ke nan cur da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace daliban ‘yan matan sakadaren a garin Chibok a jihar Borno.
(last modified 2018-08-22T06:58:08+00:00 )
Apr 14, 2016 06:33 UTC
  • shekaru biyu da sace \'yan matan Chibok
    shekaru biyu da sace \'yan matan Chibok

Yau shekaru biyu ke nan cur da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace daliban ‘yan matan sakadaren a garin Chibok a jihar Borno.

A ranar 14 ga watan afrilun shekara ta 2014 ne dai ‘yan kungiyar ta Boko Haram suka kai hari a garin Chibok, inda suka yi awun gaba da ‘yan mata 276, amma daga bisani 57 daga cikinsu suka yi nasarar tserewa daga hannun maharan.

Sace ‘yan matan Chibok sama da 200 dai ya ja hankalin al’ummar duniya

Iyayen Matan sun shirya gudanar da addu’o’I a Makarantar Chibok a yau da ake cika shekaru biyu.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Amnesty International ta wallafa rahoto da ke cewa sama da mata 2,000 kungiyar Boko Haram ta sace a Najeriya tun farkon 2014.