-
Ana Ci Gaba Da Zanga-zangar Neman Sakin Shugaban Harkar Musulunci A Najeriya.
Oct 23, 2017 15:57A jiya juma'a mambobin harkar musulunci ta Najeriya suka yi Zanga-zanga a birnin Sokoto suna masu yin kira a saki jagoransu Sheikh Ibrahmi Yakub Elzakzaky.
-
Hare-Haren Ta'addanci A Birnin Maiduguri Ya Jawo Asarar Rayuka Akalla 13
Oct 23, 2017 02:58Akalla mutane 13 ne aka tabbatar da mutuwarsu a hare-haren kunar bakin wake da aka kai a tashar Muna da ke cikin birnin Maiduguri na Jihar Borno a tarayyar Nigeria.
-
Hukumar Zaben Nigeria: Mai Yiwuwa Yawan Wadanda Suka Cancanci Kada Kuri'a A Shekara Ta 2019 Ya Kai Miliyon 80
Oct 23, 2017 02:56Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Nigeria INEC ta bada sanarwan cewa mai yiwuwa yawan wadanda suka cancanci kada kuri'a a kasar nan da shekara ta 2019 ya kai miliyon 80.
-
Gwamnatin Tarayyar Nigeria Ta Kwace Asusun Bankuna Miliyon 15 Saboda Rashin BVN
Oct 22, 2017 08:23Gwamnatin tarayyar Nigeria ta bada sanarwan kwace ususun ajiyar bankuna fiye da kimani million 15 saboda rashin BVN ko kuma lambar tantancewa ta banki.
-
Shugaba Buhari Yayi Kira Ga Hadin Kai Da Aiki Tare Tsakanin Kasashen Kungiyar D-8
Oct 20, 2017 13:48Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya kirayi shugabannin kasashen kungiyar D-8 da suke taro a kasar Turkiyya da su dau matakan da suka dace wajen kara karfafa alaka ta kasuwanci da zuba jari tsakanin kasashe membobin kungiyar.
-
Nigeria Da Turkiya Sun Amince Kan Aiki Tare Don Fada Da Ayyukan Ta'addanci
Oct 20, 2017 08:33Shugaban tarayyar Nigeria Muhammadu Buhari wanda yake ziyarar aiki a birnin Ankara na kasar Turkiya ya gana da takwaransa na kasar Turkiya Rajab Tayyeeb Erdogan inda shuwagabannin biyu suka amince da taimakawa juna don yaki da ayyukan ta'addanci da ke addabar su
-
An Rufe Makarantu A Jihar Borno Sanadiyyar Tsorin Iyayen Yara Ga Rigakafin Cutar Kyandar -Biri
Oct 20, 2017 08:27Gwamnatin jihar Borno a arewa maso gabacin tarayyar Nigeria ta bada umurnin rufe makarantun gwamnati guda 37 a birnin Maiduguri sanadiyyar jita-jitan da aka yada na cewa anawa yara riga kafin cutar kyandar-biri mai kisa.
-
Nijeriya Ta Tura Jigaren Yaki A Jihar Filato
Oct 19, 2017 13:53Rundinar sojin saman Nijeriya ta tura jiragen yaki zuwa Jos babban birnin Jihar Filato a wani mataki na dakile sabon rikicin dake neman kunno kai a yankin.
-
Shugaba Buhari Ya Amince Da Biyan Fensho Na Tsoffin Yansandan Biafara
Oct 19, 2017 08:16Shugaban tarayyar Nigeria Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan takardun amincewa da biyan tsoffin yansanda na tsohuwar kasar Biafara wacce ta yi kokaren bellewa daga kasar a shekara 1967.
-
Nigeria:Wata Jami'ar Horar Da Likitoci Zata Fara Karantar Da Ilmin Magungunan Gargajiya
Oct 19, 2017 08:15Wata jami'ar horar da likitoci a jihar Ondo na tarayyar Nigeria ta samar da fanni mai zaman kansa don karantar da ilmin magungunan garjiya