Shugaba Buhari Ya Amince Da Biyan Fensho Na Tsoffin Yansandan Biafara
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25039-shugaba_buhari_ya_amince_da_biyan_fensho_na_tsoffin_yansandan_biafara
Shugaban tarayyar Nigeria Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan takardun amincewa da biyan tsoffin yansanda na tsohuwar kasar Biafara wacce ta yi kokaren bellewa daga kasar a shekara 1967.
(last modified 2018-08-22T07:00:51+00:00 )
Oct 19, 2017 08:16 UTC
  • Shugaba Buhari Ya Amince Da Biyan Fensho Na Tsoffin Yansandan Biafara

Shugaban tarayyar Nigeria Muhammadu Buhari ya rattaba hannu kan takardun amincewa da biyan tsoffin yansanda na tsohuwar kasar Biafara wacce ta yi kokaren bellewa daga kasar a shekara 1967.

A wata sanarwa wacce Diractan hukumar Pension PTAD ya sanyawa hannu a jiya Laraba a Abuja ta bayyana cewa duk tare da cewa an yiwa tsoffin yansandan Biafara afwa tun shekara ta 2000 amma ba'a biyasu kudadensu na Pension ba shekaru bayan haka.

A tsakanin wata Yulin shekara ta 1967 zuwa Jenerun shekara ta 1970 aka yi yakin basasa a tarayyar Nigeria, inda mutanen yankin kudu maso gabacin kasar suka yi kokarin bellewa daga tarayyar Nigeria. Amma bayan an sami nasara a kansu ne gwamnatin kasar ta kori dukkan sojoji da yansanda wadanda suka bada hadin kai ga tsohuwar kasar Biafara. Sai dai a shekara ta 2000 tsohon shugaban kasar Nigeria Olusegun Obasanjo yayi masu afawa. Sai dai kuma hakan bai sa aka biyasu kudaden sallamarsu ba har zuwa yanzun da shugaban Buhari ya amince da hakan. A halin yanzu dai wadanda basa da rai danginsu zasu amshi kudaden.