Gwamnatin Tarayyar Nigeria Ta Kwace Asusun Bankuna Miliyon 15 Saboda Rashin BVN
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25110-gwamnatin_tarayyar_nigeria_ta_kwace_asusun_bankuna_miliyon_15_saboda_rashin_bvn
Gwamnatin tarayyar Nigeria ta bada sanarwan kwace ususun ajiyar bankuna fiye da kimani million 15 saboda rashin BVN ko kuma lambar tantancewa ta banki.
(last modified 2019-08-10T10:24:46+00:00 )
Oct 22, 2017 08:23 UTC
  • Gwamnatin Tarayyar Nigeria Ta Kwace Asusun Bankuna Miliyon 15 Saboda Rashin BVN

Gwamnatin tarayyar Nigeria ta bada sanarwan kwace ususun ajiyar bankuna fiye da kimani million 15 saboda rashin BVN ko kuma lambar tantancewa ta banki.

Jaridar Tribune ta Nigeria ta nakalto majiyar ofishin alkalin alkalai na kasar a Abuja na cewa dukkan wadanda abin ya shafa ba za su iya fitar da kudade ba ko kuma aika da kudade zuwa wani asusu ba. 

Hukumar kula da kula da lamuran tsakanin bankuna the Nigeria Inter Bank Settlement System Plc (NIBSS), ta ce ana da asusan ajiya a bankunan kasar kimani milliyon 45.85 amma miliyon 30,511,506 sun karbi lambar BVN har zuwa ranar 8 ga watan Oktoban shekara ta 2017.

Alkalin alkalai na kasa Justice Abubakar Malami (SAN) ne ya bukaci dukkan bankunan da abin ya shafa su toshe asusun wadanda basa da numban BVN kuma masu wadan nan asusan ajiya su je bankunan da suka bude asusun nasu kafin nan da kwanaki 14 ko kuma kudaden da suke cikinsu su zama na gwamnatin tarayyar. Yawan kudaden da rufewar asusun zata shafa dai sun kai billiyoyin Naira.