Nijeriya Ta Tura Jigaren Yaki A Jihar Filato
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i25041-nijeriya_ta_tura_jigaren_yaki_a_jihar_filato
Rundinar sojin saman Nijeriya ta tura jiragen yaki zuwa Jos babban birnin Jihar Filato a wani mataki na dakile sabon rikicin dake neman kunno kai a yankin.
(last modified 2018-08-22T07:00:51+00:00 )
Oct 19, 2017 13:53 UTC
  • Nijeriya Ta Tura Jigaren Yaki A Jihar Filato

Rundinar sojin saman Nijeriya ta tura jiragen yaki zuwa Jos babban birnin Jihar Filato a wani mataki na dakile sabon rikicin dake neman kunno kai a yankin.

A sanarwar da rundinar ta fitar ta ce ta aike da jirgin sama samfurin L-39ZA da kuma jirgi mai saukar angulu samfurin EC-135, wadanda za su bayar da kariya ga rundunar da ke aikin tabbatar da zaman lafiya a jihar, wanda kuma ba shi ne irinsa na farko ba da rundinar ta yi hakan zuwa wani yanki don tabbatar da zaman lafiya.

A ranar Litini data gabata mutane 29 ne suka gamu da ajalinsu a wani hari da aka kai masu a wata makaranta firamary inda suka nemi mafaka.

Shugaban kasar dai Muhamadu Buhari ya kwatanta rikicin jihar Filato da rashin hankali tare da shan alwashin magance shi, ta hanyar umurtar sojojin kasar su dauki matakin da ya dace don kawo karshen tashe-tashen hankula da ake samu a wasu sassan jihar.