-
Syria: "Yan ta'adda Sun Fasa Bututun Da Ke Bai Wa Damashqa Ruwa
Jul 24, 2016 14:37Shugaban Hukumar Samar Da Ruwan Sha Na birnin Damascussa a Kasar Syria, ya ce 'yan ta'adda sun fasa bututun da ke bai wa birnin Bagadaza ruwan sha.
-
Masarautar Ali-Saud Ta Haramta Wa Maniyyatan Syria Zuwa Aikin Hajjin Bana
Jul 22, 2016 12:34Sarakunan masarautar iyalan gidan Saud sun hana musulmi maniyyata daga kasar Syria zuwa aikin bana, ta hanyar hana su izinin shiga kasar (visa) ba tare da bayyana wani dalili na yin hakan ba.
-
Majalisar Dinkin Duniya Ta Bukaci Dakatar Da Bude Wuta A Arewacin Kasar Siriya
Jul 21, 2016 13:33Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci dakatar da bude wuta a lardin Halab da ke arewacin kasar Siriya tsakanin sojojin gwamnatin da gungun 'yan ta'adda da nufin samun damar isar da kayayyakin jin kai a yankunan lardin.
-
Sojojin Syria Suna Ci Gaba Da Kwace Yankunan Da Suka Rage A Hannun 'Yan Ta'adda A Aleppo
Jul 18, 2016 05:38Dakarun gwamnatin kasar Syria suna ci gaba da kara nausawa a cikin yankunan gundumar Aleppo da ke hannun 'yan ta'adda a daidai lokacin da Turkiya ta shagaltu da batun juyin mulki.
-
Syria Ta Mayar Wa Babban Sakataren Kungiyar Kasashen Larabawa Da Martani
Jul 16, 2016 06:10Ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta mayarwa babban sakataren kungiyar kasashen larabawa da martani, dangane da furucin da ya yi kan yiwuwar komawar Syria a cikin kungiyar idan ta cika sharuddan da suke bukata.
-
Adel Jubair: Dole Ne Mu Kakkabe Hannun Assad Daga Duk Wata Gwamnati Da Za A Kafa A Syria
Jul 14, 2016 23:57Ministan harkokin wajen masarautar Saudiyya Adel Jubair ya sake nanata kamalan da aka saba ji daga bakinsa dangane da makomar shugaba Bashar Assad na Syria a siyasance, inda ya ce za su kakkabe hannun Assad daga duk wata gwamnatin rikon kwarya da za a kafa a nan gaba a Syria.
-
Kasashe Turai Da Suke Goyon Bayan 'Yan Ta'adda Yanzu Suna Dandana Kudarsu
Jul 13, 2016 01:24Jakadan Kasar Siriya a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Wasu Kasashen yammacin Turai da suke goyon bayan ayyukan ta'addanci, a halin yanzu suke dandana kudarsu daga ayyukan na ta'addanci.
-
Sabuwar Majalisar Ministocin Syria Ta Yi Rantsuwar Kama Aiki A Yau
Jul 11, 2016 11:55Sabuwar Majalisar ministocin kasar Syria ta yi rantsuwar kama aiki a yau a gaban shugaba Bashar Assad, tare da halartar sabon firayi minista da kuma sauran dukkanin ministoci.
-
Sojojin Gwamnatin Siriya Sun Halaka 'Yan Ta'adda Da Dama A Yankunan Kasar
Jul 10, 2016 06:40Dauki ba dadi tsakanin sojojin gwamnatin Siriya da gungun 'yan ta'adda a yankunan da dama na kasar ya yi sanadiyyar halakar 'yan ta'adda kimanin 30.
-
An kara Tsagaita Wuta A Syria
Jul 10, 2016 01:17Rundinar sojin kasar Syria ta sanar da kara tsagaita wuta har zuwa ranar Talata mai zuwa.