Syria Ta Mayar Wa Babban Sakataren Kungiyar Kasashen Larabawa Da Martani
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta mayarwa babban sakataren kungiyar kasashen larabawa da martani, dangane da furucin da ya yi kan yiwuwar komawar Syria a cikin kungiyar idan ta cika sharuddan da suke bukata.
Bayanin ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Syria ya ce Syria ba ta da bukatar komawa a cikin kungiyar kasashen larabawa, matukar dai kungiyar za ta ci gaba da kasancewa a karkashin tasirin wasu 'yan tsirarun kasashe da ke juya ta yadda suka ga dama da kudin man fetur, maimakon ta zama kungiya mai cin gishin kanta.
Bayanin ya ce wasu kasashe masu karfin fada a ji a cikin kungiyar kasashen larabawan su ne suke iko da ita, sauran kasashen kuma sun zama 'yan amshin shata, domin kuwa da sunan kungiyar kasashen larabawa ne ake haifar da fitintinu a cikin kasashen larabawa, da sunanta ne aka kirkiro kungiyoyin 'yan ta'adda ake ba su halasci domin rusa wasu kasashen larabawa da na musulmi, matukar dai ba su dasawa da kasashen da ke juya kungiyar daidai da siyasarsu, kamar yadda suka yi a kan Syria, Libya da kuma Iraki.