An kara Tsagaita Wuta A Syria
Jul 10, 2016 01:17 UTC
Rundinar sojin kasar Syria ta sanar da kara tsagaita wuta har zuwa ranar Talata mai zuwa.
Tun da farko dai an tsagaita wutar ne a daren karama sallah Azumi domin baiwa al'umma damar gudanar da shagulgulan sallar cikin walwala.
Amma yanzu rundinar sojojin kasar ta ce an kara tsawaita tsagaita wuta har tsawan sa'o'i 72, a cewar kanfaninin dillancin labaren kasar SANA.
Gwamnatin Amurka dake aiki kafada da kafada da gwamnatin kasar Rasha domin ganin an kawo karshen zubar da jini a wannan kasa ta Syria na maraba da wannan matakin.
A halin da ake ciki sojojin Syria na ci gaba da samun galaba a kokarin da suke na tsarkake duk yankunan dake hannun 'yan tawayen kasar.
Tags