Sabuwar Majalisar Ministocin Syria Ta Yi Rantsuwar Kama Aiki A Yau
Sabuwar Majalisar ministocin kasar Syria ta yi rantsuwar kama aiki a yau a gaban shugaba Bashar Assad, tare da halartar sabon firayi minista da kuma sauran dukkanin ministoci.
Kamfanin dillancin labaran SANA na kasar Syria ya bayar da rahoton cewa, sabuwar majalisar ministocin dai ta kunshi ministoci 31, inda a ka canja 18 daga cikin ministocin kasar, yayin da sauran kuma suka ci gaba da zama kan mukamansu.
Daga cikin ministocin da aka canja kwa har da na tattalin arziki, ilimi, sadarwa, yada labarai da wutar lantarki, daga cikin ministocin da suka ci gaba da zama kan mukamansu kuwa har da na harkokin waje, cikin gida, tsaro.
Kasar Syria dai ta kwashe tsawon shekaru 5 a jere tana fuskantar matsaloli na tsaro, sakamakon ayyukan ta'addanci da kungiyoyin takfiriyyah wahabiyyah da kasashen larabawa musamman Saudiyya da Qatar gami da Turkiya da kuma Jordan suke daukar nauyinsu, da nufin kifar da gwamnatin Bashar Assad sakamakon sabanin mahangar siyasa da ke tsakaninsu da shi.