-
Sojin Siriya Sun Yi Wa Yankin Al-Mayadeen Kawanya
Oct 13, 2017 05:42Dakarun Sojin Siriya sunyi wa yankin Al-Mayadeen kawanya a wunkurin da suke na kwato yankin dake zaman sansani na karshe da kungiyar 'yan ta'adda ta IS ke rike da a gabashin kasar.
-
Siriya : IS Ta Dauki Alhakin Kai Jerin Hare-haren Damascos
Oct 11, 2017 18:18Kungiyar 'yan ta'adda ta IS ko kuma Da'esh ta ce ita keda alhakin kai jerin hare-haren kunar bakin waken da aka kai a barikin 'yan sanda Birnin Damascos.
-
Jami'an Tsaron Iran Sun Dakile Kokarin 'Yan Ta'adda Na Kai Hare-Hare Lokacin Ashura
Oct 10, 2017 05:52Ministan tsaron cikin gida da tattaro bayanan sirri na kasar Iran Sayyid Mahmoud Alawi ya bayyana cewar jami'an tsaron Ma'aikatar tasa sun sami nasarar dakile wani shiri na kai hare-haren ta'addanci a cikin Iran lokacin Ashura yana mai cewa jami'an tsaron sun kame wani adadi na 'yan ta'addan.
-
Aljeriya Ta Gabatar Da Shawara Kan Hanyar Da Ta Dace Abi A Fagen Yaki Da Ta'addanci
Oct 08, 2017 12:24Wakilin kasar Aljeriya a Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa: Kamata ya yi duniya ta bullo da wani shirin siyasa mai karko da nufin kawo karshen ayyukan ta'addanci a duniya.
-
Siriya : Sojin Rasha Sun Hallaka 'yan Ta'addan (IS) 120
Oct 07, 2017 10:57Ma'aikatar tsaron kasar Rasha ta sanar da cewa dakarunta sun hallaka 'yan ta'addan da'esh 120 a wani harin sama da aka kai masu.
-
Nijer : Ana Zaman Makoki Na kwanaki 3 Bayan Kisan Sojoji
Oct 07, 2017 10:57A Nijar an fara wani zamen makoki na kwanaki tun daga jiya Juma'a, bayan kisan wasu sojojin kasar hudu da na Amurka da wasu mahara daga Mali sukayi a tsakiyar wannan mako.
-
Siriya : IS Ta Dauki Alhakin Kai Harin Da Ya Yi Ajalin Mutum 17 A Damascos
Oct 03, 2017 10:52Kungiyar 'yan ta'adda ta Da'esh wato IS ta ce ita ke da alhakin kai harin da ya yi ajalin mutum 17 a birnin Damascos na kasar Siriya.
-
Bayan Hukumcin Kotu, Gwamnatin Nijeriya Ta Ayyana Kungiyar IPOB A Matsayin Kungiyar Ta'addanci
Sep 21, 2017 05:46Bayan hukumcin da wata babbar kotun Abuja ta fitar na haramta ayyukan kungiyar IPOB ta masu fafutukar kafa kasar Biafra, gwamnatin Nijeriya ta ayyana kungiyar a matsayin kungiyar 'yan ta'adda.
-
Najeriya : Mutum 15 Sun Mutu A Hare-haren Kunar Bakin Wake
Sep 18, 2017 14:04Rahotanni daga Najeriya na cewa mutane a kalla 15 ne suka rasa rayukansu a wasu jerin hare haren kunar bakin wake a wani sansanin 'yan gudun hijira dake kauyen Mashahari na birnin Maiduguri a arewa maso gabashin kasar.
-
Biritaniya : Ana Farautar Maharan Landan
Sep 16, 2017 05:44'Yan sanda a Biritaniya sun ce suna ci gaba da farautar mutanen dake hannu a harin da aka kai a wata tashar jirgin kasa a birnin Landan.