Nijer : Ana Zaman Makoki Na kwanaki 3 Bayan Kisan Sojoji
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i24721-nijer_ana_zaman_makoki_na_kwanaki_3_bayan_kisan_sojoji
A Nijar an fara wani zamen makoki na kwanaki tun daga jiya Juma'a, bayan kisan wasu sojojin kasar hudu da na Amurka da wasu mahara daga Mali sukayi a tsakiyar wannan mako.
(last modified 2018-08-22T11:30:48+00:00 )
Oct 07, 2017 10:57 UTC
  • Nijer : Ana Zaman Makoki Na kwanaki 3 Bayan Kisan Sojoji

A Nijar an fara wani zamen makoki na kwanaki tun daga jiya Juma'a, bayan kisan wasu sojojin kasar hudu da na Amurka da wasu mahara daga Mali sukayi a tsakiyar wannan mako.

Gwamantin Nijar ta sanar da hakan ne a yayin wani taron ministocinta na mako mako a jiya, inda ta isar da ta'aziyyarta ga iyalan sojojin da suka rsa rayukansu a harin kwantan baunan da aka kai masu a kusa da kan iyaka da kasar Mali.

Ma'aikatar tsaron Amurka ta Pentagon ta sanar da cewa sojojinta hudu suka gamu da ajaliinsu a harin.

Wannan lamari dai ya tabbatar da kasancewar sojin Amurka a wannan kasa ta Nijar.