Sep 16, 2017 05:44 UTC
  • Biritaniya : Ana Farautar Maharan Landan

'Yan sanda a Biritaniya sun ce suna ci gaba da farautar mutanen dake hannu a harin da aka kai a wata tashar jirgin kasa a birnin Landan.

Harin na jiya wanda aka kai a tashar jirgin kasa Parsons Green station a Fulham ya dai yi sanadin jikaktar mutane 29.

kwamandan 'yan sandan yankin Mark Rowley ya shaida a wani taron manema labarai da yammacin jiya cewa suna neman wasu mutane, aman duk da hakan ya ce akwai ci gaba sosai a binciken da ake yi.

Binciken dai a cewarsa ya gano cewa wani mutum ne ya ajiye wani abu mai fashewa a cikin jirgin, wanda ya tabbatar da cewa harin ta'addanci ne.

A halin da ake ciki dai kungiyar 'yan ta'dda ta IS, ta fitar da sanarwa ta hanyar shafin yada farfagandan ta na Amaq cewa ita ke da alhakin kai harin.

Tags