Pars Today
Hukukoni a Burkina Faso, sun ce makarantun boko sama da dudu guda ne suka rufe kokofinsu ko kuma suka dakatar da koyarwa a jihohi biyar na kasar, saboda barazanar mayakan dake ikirari da sunan jihadi.
Majalissar dokokin kasar Masar, ta amince da kara wa'adin dokar ta baci a wasu yankunan kasar da watanni uku.
Shugaban kasar Uganda ya bayyana cewa: Gwamnatinsa zata dauki tsauraran matakan shawo kan matsalolin tsaro da suke addabar kasar tare da hukunta masu hannu a gudanar da ayyukan ta'addanci a kasar.
Gwamnatin kasar Libiya ta sanar da sanya hannu kan yarjejjeniyar tsaro na kare iyakokin kasar da kasashen Nijar, Sudan da Chadi.
Gwamnatin Tunusiya ta tsawaita da watanni bakwai dokar ta baki a fadin kasar.
Kakakin rundunar sojin Masar ya sanar da cewa: Jami'an tsaron kasar sun karfafa matakan tsaro a dukkanin yankunan da majami'un kasar suke da nufin bai wa mabiya addinin kirista tsaro a lokacin bukukuwan shiga sabuwar shekara ta 2018.
Rahotanni daga Kamaru na cewa jami'an tsaron kasar na Jandarma hudu ne suka rasa rayukansu a wani hari da aka kai masu a yankin masu magana da harshen turancin Ingilishi a Kudu maso yammacin kasar.
Halartar shuwagabannin kasashen duniya daban daban da kuma shuwagabannin kungiyoyin kasa da kasa a bikin rantsar da Dr Hassan Ruhani a matsayin shugaban kasar Iran karo na biyu yana nuna irin matsayin da Iran take da shi a yankin gabas ta tsakiya da kuma duniya gaba daya.
Kasashen Iran da Iraki sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimtar juna da aiki tare a bangarorin tsaro da aikin soji a kokarin da ake yi na karfafa yanayin tsaron kasashen biyu da kuma yankin Gabas ta tsakiya
Masar Ta fitar da daliban jami'ar nan guda 4 'yan kasar Indanosiya da ta zarga da kokarin tayar da hankali