Burkina Faso : An Rufe Makarantu Dubu Saboda Barazanar Tsaro
Hukukoni a Burkina Faso, sun ce makarantun boko sama da dudu guda ne suka rufe kokofinsu ko kuma suka dakatar da koyarwa a jihohi biyar na kasar, saboda barazanar mayakan dake ikirari da sunan jihadi.
Da yake sanar da hakan ministan yaki da jahilci na kasar, Stanislas Ouaro, ya ce ye zuwa ranar 15 ga watan Fabrairun nan na 2019, makarantun boko dubu da dari da talatin da biyar ne (1,135), ne suka bar aiki, lamarin da a cewarsa ya raba yaradalibai dubu dari da hamsin da dari da talatin da uku (154,233), da 'yancin samun ilimi.
Mista Ouaro, ya kara da cewa kashin 46% na yaran makaranta da lamarin ya shafa 'ya 'ya mata ne, lamarin da ya tabbatar da alkalumman da MDD, ta fitar a makon da ya gabata.
Hukumonin a kasar sun ce, barazanar da harkar ilimi ke fuskanta a kasar tun shekara 2016, ta kazanta tun a bara, musamman a yankunan Sum da Yatenga da kuma Lorum dake arewacin kasar, kana kuma lamarin ya kara yin muni a bana inda ya bazu zuwa wasu sassan gabashi, da tsakiya.
Matsalar tsaro mai nasaba da mayakan dake ikirari da sunan jihadi da kasar Burkina Faso, ke fuskanta yau da shekaru hudu a arewacin kasar ta bazu a baya bayan nan zuwa babban birnin kasar da kuma wasu sauren jihohi musamman na gabashi.
Kafin hakan dama wasu alkalumma da ofishin kula da ayyukan jin kai na MDD, (OCHA), ya fitar, ya yi gargadin cewa mutane miliyan 1,2 ne ke bukatar agajin gaggawa sakamakon matsalar tsaro a wannan kasa ta Burkina Faso.