Masar Ta Kori Daliban Indosiya 4
Masar Ta fitar da daliban jami'ar nan guda 4 'yan kasar Indanosiya da ta zarga da kokarin tayar da hankali
A wata sanarwa da ya fitar a wannan Assabar, Jakadan kasar Indanosiya dake birnin Alkahira ya tabbatar da cewa Daliban kasar sa da jami'an tsaron kasar Masar suka kame a watan jiya an mayar da su gida a yau din nan.
A ranar 6 ga watan yunin da ya gabata ne jami'an tsaron kasar Masar suka cabke wasu daliban jami'a 'yan kasar Indanosiya dake karatu a cikin kasar guda 4,bayan da aka bayyana su a matsayin hadari na tsaron kasar.
Ofishin Jakadancin Indanosiya a birnin Alkahira ya ce har yanzu Gwamnatin Masar ba ta basu dalilan da ya sanya ta kama daliban kasar dake da izinin takardun zama a cikin kasar ba.
Kafin hakan dai, Hamli Fauzi jakadan indonesia dake birnin Alkahira ya yi watsi da zarkin da magabatan kasar Masar din suka yiwa daliban.