An Tsawaita Dokar Ta Baci Da Watanni 7 A Tunusiya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i28869-an_tsawaita_dokar_ta_baci_da_watanni_7_a_tunusiya
Gwamnatin Tunusiya ta tsawaita da watanni bakwai dokar ta baki a fadin kasar.
(last modified 2018-08-22T11:31:31+00:00 )
Mar 07, 2018 05:47 UTC
  • An Tsawaita Dokar Ta Baci Da Watanni 7 A Tunusiya

Gwamnatin Tunusiya ta tsawaita da watanni bakwai dokar ta baki a fadin kasar.

A cen baya hukumomin kasar kan tsawaita wannan dokar ce daga wata guda zuwa uku, saidai a wannan karon farko an tsawaita dokar da watanni bakwai.

Dokar dai kan baiwa jami'an tsaro ikon tabbatar da tsaro ta ko wanne irin hali, ba sani-ba sabo, tana kuma da karfin haramta zanga-zanga a fadin kasar, data fuskanci jerin hare haren ta'addanci a cen baya.

'Yan Tunusiya da dama dai na ganin dokar bata kawo wani sauyi na azo a gani ba.

Marabin da Tunusiya ta fuskanci wani harin ta'addanci tun cikin shekara 2016, wanda hakan a cewar hukumomin kasar alama ce ta samun babbar nasara a sha'anin tabbatar da tsaro, da kuma sanya ido akan abubuwan dake wakana a kasar Libiya dake fama da matsalar tsaro.