Pars Today
Kotun koli a kasar Holland ta bayar da umarni da a gina ma musulmi makarantar sakandare a cikin birnin Amstardam fadar mulkin kasar.
Wasu kasashen Yammacin Turai da na Afrika sun cimma yarjejeniyar bin hanyoyin da suka dace domin kalubalantar matsalar kwararan bakin haure zuwa kasashen Turai musamman ta hanyar teku.
Taron dai an yi shi ne a tsakanin ministocin wajen kasashen nahiyoyin biyu a birnin Rom na kasar Italiya a yau alhamis.
Ministan harkokin wajen kasar Iran Muhammad jawad zarif ya bayyana cewa, mayar da yankin gabas ta tsakiya wata kasuwar sayar da makamai, ba zai haifar ma yankin da mai ido ba.
Majlaisar musulmin kasar Birtaniya ta bukaci mahukuntan kasar da su dauki matakan kare wuraren ibada da suka hada da masallatai da kuma cibiyoyin musulmi.
Kungiyar tarayyar Turai EU ta gargadi kasashen Hungary, Poland da kuma Jumhuriyar Czech saboda kin karban masu neman mafaka da suka yi, wanda hakan ya sabawa dokokin tarayyar kuma tana iya daukar mataki a kansu.
Kasar Jamus wacce ke rikeda shugabannin kungiyar kasashe mafi arziki a duniya na G20 na son karfafa alakar kasuwanci ta hanyar zuba jari a nahiyar Afrika a wani mataki na yaki da kwararar bakin haure.
An Gudanar da taron Ministocin Harakokin wajen kasashen Afirka da arewacin Kasashen Turai a birnin Abuja fadar milkin Najeriya.
Babbar jami'ar harkokin wajen kungiyar tarayyar turai Federica Mogherini ta bukaci a kafa Rundunar tsaron hadin gwiwa na kasashen yankin Sahel domin yaki da ta'addanci
Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta kasar Spain ta lashe gasar zakaran zakarun Turai bayan ta doke kungiyar kwallon kafa ta Juventus ta kasar Italiya da ci 4-1 a wasan karshen da suka buga a birnin Cardiff da ke Birtaniya a daren jiya Asabar.