Taron Ministocin Harakokin Wajen Kasashen Afirka A Najeriya
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i21200-taron_ministocin_harakokin_wajen_kasashen_afirka_a_najeriya
An Gudanar da taron Ministocin Harakokin wajen kasashen Afirka da arewacin Kasashen Turai a birnin Abuja fadar milkin Najeriya.
(last modified 2019-01-16T07:30:45+00:00 )
Jun 10, 2017 11:53 UTC
  • Taron Ministocin Harakokin Wajen Kasashen Afirka A Najeriya

An Gudanar da taron Ministocin Harakokin wajen kasashen Afirka da arewacin Kasashen Turai a birnin Abuja fadar milkin Najeriya.

Kamfanin dillancin labaran Irna ya habarta cewa a jiya Juma'a, an gudanar da taron hadin gwiwa tsakanin ministocin harakokin waje na kasashen Afirka da arewacin kasashen Turai karo na 16 a birnin Abuja fadar milkin Najeriya, taron na bana dai an bashi taken (Tabbatar da ci gaba mai dorewa ta hanyar zuba jari) da nufin karfafa shawarwarin Siyasa tsakanin kasashen Afirka da kasashen  arewacin Nahiyar Turai.

A yayin wannan zama, mahalarta taron sun tattauna kan batutuwan da suka shafi zuba hannun jari, kafa kamfanoni, musayar kasuwanci tsakanin kasashen Afirka da kasashen Arewacin nahiyar Turai tare kuma da batun tabbatar da tsaro da sulhu a tsakanin kasashen.