G20 / Afirka : Merkel Za Ta Gana Da Wasu Shugabannin Afrika
(last modified Mon, 12 Jun 2017 05:44:28 GMT )
Jun 12, 2017 05:44 UTC
  • G20 / Afirka :  Merkel Za Ta Gana Da Wasu Shugabannin Afrika

Kasar Jamus wacce ke rikeda shugabannin kungiyar kasashe mafi arziki a duniya na G20 na son karfafa alakar kasuwanci ta hanyar zuba jari a nahiyar Afrika a wani mataki na yaki da kwararar bakin haure.

Yau Litinin ce shugabar gwamnmatin Jamus Angela Merkel za ta fara ganawa da wasu shugabannin Afrika a birnin Berlin da nufin karfafa alaka ta fannonin ci gaban tattalin arziki mai daurewa a Afirka.

Ganawar ta Mme Merkel da shugabannin Afrikar na zuwa ne a yayin da ya rage kasa da wata guda a gudanar da babban taron kasashen mafi arziki na G20 a Hambourg.

Shugabannin kasashen Afrika da zasu ganawa da Mme Merkel a taron na Barlin na kwanaki biyu sun hada dana Ghana, Habasha, Nijar, Masar da kuma Mali.

Dama kafin hakan shugabar bankin bada lamuni na duniya (IMF) wato Christine Lagarde ta ce zasu lalubo hanyoyin samar da tallafi a kasashen kudancin Afrika domin mutanen yankin su zauna gida don tsayawa da kafafunsu domin kula da iyalensu.