Taro A Tsakanin Wakilan Nahiyoyin Turai Da Afirka Akan "Yan Hijira.
(last modified Thu, 06 Jul 2017 18:58:57 GMT )
Jul 06, 2017 18:58 UTC
  • Taro A Tsakanin Wakilan Nahiyoyin Turai Da Afirka Akan

Taron dai an yi shi ne a tsakanin ministocin wajen kasashen nahiyoyin biyu a birnin Rom na kasar Italiya a yau alhamis.

Taron dai an yi shi ne a tsakanin ministocin wajen kasashen nahiyoyin biyu a birnin Rom na kasar Italiya alhamis.

Ministan harkokin wajen kasar Italiya Angelo Alfano ya ce; Mnaufar taron da su ka yi a yau din shi ne tattauna matsalar da ake fuskanta ta 'yan ci-rani, kuma ci gaba ne da taron da aka yi a kasar Estonia.

Daga nahiyar Afirka an sami halartar ministocin harkokin wajen kasashen Libya, Nijar, Tunisiya, Masar, Chadi, Habasha da kuma Sudan. Dukkanin ministocin sun rattaba hannu akan fahimta ta baidaya.

Tun daga 2015 zuwa yanzu, an fada cikin matsalar yan ci rani mafi girma a duniya inda dubbai su ke mutuwa ta hanyar nutsewa a ruwa akan hanyarsu ta zuwa turai.