Pars Today
Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya kirayi shugabannin kasashen kungiyar D-8 da suke taro a kasar Turkiyya da su dau matakan da suka dace wajen kara karfafa alaka ta kasuwanci da zuba jari tsakanin kasashe membobin kungiyar.
Sakatarorin harkokin wajen kasashen Amurka da Rasha sun tattauna ta wayar tarho kan takaddamar data kunno bayan soke bada bisa tsakanin kasashen biyu.
Shugabannin kasashen Iran da Turkiyya sun bayyana cewa ba za su taba amincewa da kokarin Kurdawa na rarraba kasar Iraki ba, suna masu sake jaddada shirin gwamnatocinsu na kara karfafa alakar da ke tsakanin kasashen biyu.
Kasashen Turkiyya Da Iran sun karfafa matakan ayyukan soji a wani mataki na tsaron iyakokinsu.
Shugaba Vladimir Putin na Rasha, zai gana da takwaransa na Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan a birnin Ankara, a yayin wata 'yar gajeriyar ziyara da ya ke a birnin Ankara.
Gwamantin Iran ta sanar da dakatar da dukkan zurga-zurga jiragan sama zuwa yankin Kurdistan na Iraki, a yayin da ake gaf da jefa kuri'ar raba gardama kan ballewar yankin na Kurdawa.
Gwamnatin kasar Turkiya ta bude wasu sabbin Ofisoshin jakadanci a wasu kasashen Afrika da zimmar fadada harkokin tattalin arziki da na siyasa da kasashen nahiyar
Shugaban kasar Turkiyya ya yi furuci da cewa: Wata kasa daga cikin kungiyar tsaro ta NATO ta taka gagarumar rawa a fagen mallaka wa kungiyar ta'addanci ta Da'ish makamai a kasashen Iraki da Siriya.
Kakakin kotunan na musamman don hukunta yan ta'adda a kasar Tuniya ya bada sanarwan cewa kotunan sun karbi yan ta'adda guda ukku daga kasar Turkiya kuma sun jefa su a cikin kurkuku a kasar.
Babban kwamandan sojojin kasar Iran Manjo Janar Mohammad Bakiri ya bayyana cewa gwamnatin kasar Iran ba ta goyon shirin Kurdawan kasar Iraki na gudanar da zaben raba gardama don warewar yankin daga kasar iraqi.