Gwamnatin Turkiya Ta Bude Sabbin Ofisoshin Jakadanci A Wasu Kasashen Afrika
Gwamnatin kasar Turkiya ta bude wasu sabbin Ofisoshin jakadanci a wasu kasashen Afrika da zimmar fadada harkokin tattalin arziki da na siyasa da kasashen nahiyar
Jaridar Daily-Sabah ta kasar Turkiya ta nakalto Elif Comoglu Ulgen jakadan kasar ta Turkiya a birnin Pretoria na kasar Afrika ta kudu yana fadar haka a ranar Laraban da ta gabata.
Ulgen ya kara da cewa kasar Turkiya zata bude ofisoshin jakadancinta a kasashen Lesotho da kuma Swazland, inda a halin yanzu ya rika ya mika bukatar hakan ga gwamnatocin kasashen biyu, sannan yana jiran amincewarsu don bude ofisoshin.
Jakadan Turkiya a Pretoria ya ce sabuwar siyasar gwamnatin kasar Turkiya ita ce fadada dangantaka da kasashen Afrika, sannan ya kara da cewa a cikin shekaru 10 da suka gabata yawan ofisoshin jakadancin Turkiya a kasashen Afrika ya ninka, inda ya tashi daga 14 zuwa 39.
Ulgen ya ce shugaban kasar Turkiya Rajab Tayyib Urdugan yana son nan gaba kadan kasar Turkiya ta kasance tana da ofishin jakadancinta a dukkanin kasashen Afrika.