Pars Today
Jagoran tawagar masu sanya ido na MDD kan rikicin Yemen ya isa Sanaa babban birnin kasar ta Yemen da 'yan Houtsie ke rikeda, bayan da ya ziyarci birnin Aden a jiya Asabar.
Kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya ya amince da tura tawagar majalisar wacce zata kula da tashar jiragen ruwa ta Al-Hudaida mai muhimmanci a kasar Yemen.
A wani lokaci yau Juma'a ne ake sa ran kwamitin tsaro na MDD, zai yi wani zama domin kada kuri'a kan kudirin tura jami'ansa masu sanya ido a kasar Yemen.
Rahotanni daga Yemen na cewa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakannin bangarorin dake rikici a kasar na tangal-tangal a arewacin Hodeida.
Majiyoyi daga MDD, sun bayyana cewa a gobe Talata ne yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin bangarorin dake rikici a Yemen zata fara aiki.
Majalisar Dinkin Duniya ta cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yankunan dake fama da rikici a Yemen, bayan tattaunawar neman zaman lafiya data gudana a Swiden tsakanin bangarorin dake rikici a kasar ta Yemen.
Jagoran juyin juya halin Musulunci a nan Iran Aya. Khaminae ya bayyana cewa gwamnatin kasar Amarka tana taimakawa gwamnatin kasar Saudia a ta'asar da take aikatawa a kasar Yemen.
A wani mataki na karfafa wa tattaunawar neman sulhu da ake tsakanin bangarorin dake rikici a kasar Yemen, sakatare Janar na MDD, Antonio Guteres, zai je Swiden domin ganawa da bangarorin da batun ya shafa.
Shugaban kasar Iran Hasan Rouhani ya bayyana goyon bayan Jamhuriyar Musulunci ta Iran ga tattaunawar sulhun kasar Yemen yana mai cewa a halin yanzu 'yan mamaya sun fahimci cewa yin sulhu da al'ummar Yemen shi ne kawai damar da suke da shi.
Majalisar Dinkin Duniya ce ta bayyana cewa mutane miliyan 10 na kasar Yemen din za su bukaci abinci a shekara mai zuwa