Yemen : Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Na Tangal-tangal a Hodeida
Rahotanni daga Yemen na cewa yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakannin bangarorin dake rikici a kasar na tangal-tangal a arewacin Hodeida.
A makon da ya gabata ne bangarorin suka cimma yarjejeniya a kasar Sweden a shiga tsakanin MDD, wacce ta tanadi tsagaita wuta a birnin Hodeida da ya kunshi tashar ruwa inda ta nan ne ake shigar da galibin kayan agaji dana abinci ga fararen hula.
Saidai yarjejeniyar wacce ta fara aiki a ranar Talata data gabata, bata hana samun fadace fadace tsakanin bangarorin biyu ba, duk da cewa an samu dan sukuni a wasu sassan birnin a baya baya nan.
Dukan bangarorin dai na zargin jinansu da keta yarjejeniyar.
Nan gaba ne ake sa ran MDD, zata aike da masu sanya ido a birnin na Hodeida kamar yadda yarjejeniyar da aka cimma ta tanada, kafin fara musayar fursunoni tsakanin bangarorin biyu dake rikici.
MDD, dai na matsin lamba ga bangarorin dasu mutunta yarjejeniyar da aka cimma a ranar 13 ga watan Disamba nan.