Dec 17, 2018 10:38 UTC
  • Ranar Talata Yarjejeniyar Tsagaita Wuta Zata Fara Aiki A Yemen

Majiyoyi daga MDD, sun bayyana cewa a gobe Talata ne yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cimma tsakanin bangarorin dake rikici a Yemen zata fara aiki.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka gwabza fada tsakanin bangarorin biyu a birnin Hodeida duk da yarjejeniyar da aka sanar an cimma tsakanin bangarorina shiga tsakanin MDD a ranar Alhamis data gabata a Swiden.

Wani jami'in MDD, da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa, yarjejeniyar tsagaitar zata fara aiki daga karfe 12 na dare ranar Talata, agogon wurin, wato karfe 9:00 na dare agogo na GMT. 

Shi ma a nasa bangare ministan harkokin wajen kasar ta Yemen, Khaled al-Yemani, ta tabbatar da hakan a wata sanarwa ta gidan talabijin din kasar, a yayin da ake sa ran masu dauke da makamai zasu fara janye wa daga birnin na Hdeida a cikin kwanaki masu zuwa, kamar yadda yarjejeniyar ta tanada.

Tags