Mutane Miliyan 10 Na Kasar Yemen Na Bukatar Taimakon Abinci
Majalisar Dinkin Duniya ce ta bayyana cewa mutane miliyan 10 na kasar Yemen din za su bukaci abinci a shekara mai zuwa
Mataimakin babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniya Mark Lowcock da ya gabatar da taron manema labaru akan batun ya kara da cewa; Ana samun karuwar tabarbarewar al'amurra a kasar Yemen, don haka muna da bukatuwa da taimakon kudade
Lowcock ya ci gaba da cewa; Majalisar Dinkin Duniya tana son ganin ta samar da abinci ga mutane kasar Yemen miliyan 15 a shekara mai zuwa
Babban magatakardar Majalisar Dinkin Duniyar Antonio Gutrress ne zai jagoranci kaddamar da gidauniyar tara kudade domin al'ummar kasar Yemen a ranar 26 ga watan Febrairu na shekara mai zuwa.
Lowcock ya kuma ce ana da bukatuwa ne da kudin da za su kai dala biliya 4 saboda tanadar abinci ga al'ummar kasar ta Yemen