-
An Gayyaci Tsohon Shugaban Gambiya Da Ya Zo Ya Ba Da Shaida A Gaban Kwamitin Bincike
Jun 02, 2018 01:01Kwamitin binciken da gwamnatin kasar Gambiya ta kafa don binciken kadarorin da tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh ya mallaka ya gayyace shi tare da iyalansa da wasu na kurkusa da shi da su bayyana a gaban kwamitin don amsa tambayoyi da kuma neman karin bayani.
-
Burundi : Kotun Tsarin Mulki Ta Yi Na'am Da Sakamakon Zaben Raba Gardama
Jun 01, 2018 09:54Kotun tsarin mulki a kasar Burundi ta tabbatar da sakamakon zaben raba gardama da aka kada kuri'arsa a ranar 17 ga watan Mayu da ya gabata, kan yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima.
-
Boko Haram Ta Kashe Sojojin Najeriya Biyar
Jun 01, 2018 09:31Rundinar sojin Najeriya ta sanar da mutuwar sojojinta biyar, a yayin da suka taka nakiya a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.
-
Wata Kotu A Kaduna Ta Jefa Tsohon Gwamnan Jihar -Yero- Cikin Kurkuku
Jun 01, 2018 07:16Wata kotun gwamnatin tarayyar a jihar Kaduna ta bada umurnin tsare tsohon gwamnan jihar Muktar Ramalan Yero a gidan yari kafin a kammala shirye shiryen bada belinsa.
-
An Fara Shirin Tube Limamai Masu Ikidar Wahhabiyanci Da Salafanci A Kasar Mauritania
Jun 01, 2018 07:15Ma'aikatar ilmi da lamuran addinin musulunci a kasar Mauritania ta fara gudanar da gyare gyare a cikin lamuran masallantai a kasar, don rage sabani da tashe tashen hankula a tsakanin musulmi.
-
Shugaban Sudan Ya Bayyana Bacin Ransa Kan Mummuanan Halin Da Tattalin Arzikin Kasarsa Take Ciki
Jun 01, 2018 07:14Shugaban kasar Sudan Umar Hassan El-Bashir ya bayyana matukar bacin ransa kan mummanan halin tattalin arzikin da kasarsa take ciki duk tare da cewa an dauke mata wasu takunkuman tattalin arzikin da aka dora mata.
-
Buhari Ya Sa Wa Dokar Bai Wa Matasa Damar Tsayawa Takara Hannu
May 31, 2018 11:29Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya sanya hannu kan sabuwar dokar nan ta bai wa matasan kasar damar tsayawa takara a zabubbukan da za a gudanar a kasar; lamarin da matasan kasar suka jima suna jira.
-
An Kai Karar Yahya Jammeh Saboda 'Maganin AIDS Na Boge'
May 31, 2018 11:29Wasu mutane guda uku da suka yi amfani da maganin cutar kanjamau (AIDS) da tsohon shugaban kasar Gambiya Yahaya Jammeh ya samar sun shigar da karar tsohon shugaban bisa zargin ya haifar musu da matsala cikin lafiyarsu.
-
Kotu A Kaduna Ta Turo Tsohon Gwamnan Jihar, Yero, Gidan Yari
May 31, 2018 11:29Wata babbar kotun tarayya a Kaduna, da ke arewacin Nijeriya ta ba da umurnin a tsare tsohon gwamnan jihar Mukhtar Ramalan Yero da wasu mutane uku a gidan yari saboda zargin cin amana da halatta kudin haram.
-
Libiya Ta Mayar Da 'Yan Ci-Rani 221 Kasashensu
May 31, 2018 05:34Mahukunta a Libiya, sun sanar da tisa keyar 'yan ci rani 'yan asalin kasashen Afrika dana Asiya su 221 zuwa kasashensu.