Buhari Ya Sa Wa Dokar Bai Wa Matasa Damar Tsayawa Takara Hannu
(last modified Thu, 31 May 2018 15:59:55 GMT )
May 31, 2018 15:59 UTC
  • Buhari Ya Sa Wa Dokar Bai Wa Matasa Damar Tsayawa Takara Hannu

Shugaba Muhammadu Buhari na Nijeriya ya sanya hannu kan sabuwar dokar nan ta bai wa matasan kasar damar tsayawa takara a zabubbukan da za a gudanar a kasar; lamarin da matasan kasar suka jima suna jira.

Rahotanni daga Nijeriyan sun ce a yau din nan Alhamis ne shugaba Buharin ya sanya hannu kan wannan dokar da a turance ake kira da dokar ‘Not Too Young To Run’ wacce ta rage shekarun mutanen da suka cancanci tsayawa takara a zabubbukan kasar kama daga shugaban kasa, gwamnoni, 'yan majalisu da sauransu.

Fadar shugaban Nijeriyan ta fitar da wasu faifan bidiyo inda shugaban yake sanya hannu kan wannan dokar wacce tun a shekarar bara ta 2017 ne Majalisar dattawan kasar ta amince da kudirin dokar da zai bai wa matasa damar tsayawa takara a mukaman shugaban kasa, gwamna da na 'yan majalisun dattawa da na wakilai na kasar. 

A bisa dokar dai an rage shekarun cancantar tsayawa takarar shugaban kasa daga shekaru 40 zuwa 35, yayin da a bangaren gwamnoni da sanatoci aka bukatar rage shekarun daga 35 zuwa 30, wanda hakan zai ba wa matasa damar tsayawa takarar.