Wata Kotu A Kaduna Ta Jefa Tsohon Gwamnan Jihar -Yero- Cikin Kurkuku
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i31322-wata_kotu_a_kaduna_ta_jefa_tsohon_gwamnan_jihar_yero_cikin_kurkuku
Wata kotun gwamnatin tarayyar a jihar Kaduna ta bada umurnin tsare tsohon gwamnan jihar Muktar Ramalan Yero a gidan yari kafin a kammala shirye shiryen bada belinsa.
(last modified 2018-08-22T07:01:54+00:00 )
Jun 01, 2018 07:16 UTC
  • Wata Kotu A Kaduna Ta Jefa Tsohon Gwamnan Jihar -Yero- Cikin Kurkuku

Wata kotun gwamnatin tarayyar a jihar Kaduna ta bada umurnin tsare tsohon gwamnan jihar Muktar Ramalan Yero a gidan yari kafin a kammala shirye shiryen bada belinsa.

Jaridar Daily Trust ta Nigeria ta bayyana cewa an gurfanar da tsohon gwamnan tare da mutane ukku wadanda suka hada da tsohon shugaban jam'iyyar PDP na jihar Abubakar Gaya Haruna, tsohon minista Nuhu Somo Wya da kuma tsohon sakataren gwamnatin jihar Hamza Ishaq kan zargin batar da kudade naira miliyon 700.

Kotun tana tuhumar wadannan tsoffin jami'an gwamnatin da almundaha da kudadi jami'a wadanda ya sabawa dokokin sarrafa kudaden jama'a a lokacin suke da iko a jihar.

Joshua Saidi, mai gabatar da kara na hukumar EFCC ya bayyana cewa hukumarsa bata da wurin ajiye su don haka alkalin ya ce a tafi da su kurkuku har zuwa ranar 6 ga watan Yuni mai kamawa, a lokacinda zai sake sauraron karar.