Boko Haram Ta Kashe Sojojin Najeriya Biyar
(last modified Fri, 01 Jun 2018 14:01:28 GMT )
Jun 01, 2018 14:01 UTC
  • Boko Haram Ta Kashe Sojojin Najeriya Biyar

Rundinar sojin Najeriya ta sanar da mutuwar sojojinta biyar, a yayin da suka taka nakiya a jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Da yake sanar da hakan wani kakakin rundinar sojin kasar, Texas Chukwu, ya ce sojojin sun rasa rayukansu ne a yayin da suka taka abubuwan masu fashewa lokacin wani sintiri a ranar Alhamis data gabata a yankin Gwaza dake jihar ta Borno. 

Kakakin rundinar ya ce, sojojin da 'yan ta'addan sun yi ba-ta-kashi sosai, an kuma  kashe mayakan na Boko Haram da dama yayin arangamar.

Sojojin sun kuma kubutar da wasu mutane tara da mayakan sukayi garkuwa dasu.

Rundinar sojin ta ce zata mika mutanen da suka hada da maza biyu, da mata biyu, da kuma yara biyar ga hukumomin Najeriya da batun ya shafa cikin gaggawa, bayan an kammala bincien kiwan lafiyarsu a wata barikin soji.