-
An Kawo Karshen Taron Shugabannin Tarayyar Afirka A Kasar Habasha
Feb 12, 2019 03:43A jiya Litinin da marece ne aka kawo karshen taron shugabannin kungiyar tarayyar Afirka karo na 32 a birnin Adis Ababa na kasar Habasha
-
Libya: Sojojin Halifa Haftar Sun Kwace Iko Da Rijiyoyin Mai Mafi Girma Na Kasar
Feb 12, 2019 03:41Kamfanin dillancin labarun Anatoli ya nakalto cewa; Bayan kwanaki da sojojin na Halifa Haftar su ka killace yankin na al'Shararah, wanda shi ne wuri mafi girma na man fetur a kasar ta Libya, a karshen sun kwace iko da shi a jiya Litinin
-
Gwamnatin Libiya Ta Bukaci Taimakon Kwamitin Sulhu Na MDD
Feb 11, 2019 16:01Gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya ta bukaci majalisar sulhu ta majalisar Dinkin Duniya da ta dauki matakin dakatar da dakarun tsaron kasar karkashin janar Khalifa Haftar ci gaba da hare-haren da suke kaiwa kudancin kasar
-
PDP Ta Yi Tsokaci Kan Gobarar Ofishin INEC
Feb 11, 2019 15:35Babbar Jam’iyyar adawa ta PDP a Najeriya ta bayyana kaduwarta game da gobarar da ta cinye kayayyakin zabe a ofishin Hukumar Zaben Kasar, INEC da ke yankin Quan Pan a Jihar Filato, in da ta bukaci a gudanar da bincike kan lamarin.
-
Kasar Masar Ta Karbi Shugabancin Karba-Karna Na Tarayyar Afrika
Feb 11, 2019 07:49Shugaban kasar Masar Abdulfattah Assisi ya karbi shugabancin karba-karba na kungiyar Tarayyar Afrika.
-
Najeriya: 'Yansanda Sun Kara Kyautata Tsaro A Dukkan Ofisoshin Hukumar Zabe A Fadin Kasa
Feb 11, 2019 07:48Spetan 'yansanda na riko a tarayyar Najeriya Mohammad Adamu ya bada umurni ga 'yansandan kasar su tabbatar da tsaro na musamman ga dukkanin ofisoshin hukumar Zaben kasar da kuma dukkan kayakin da suka shafe zabe a duk fadin kasar.
-
SADC Da MDD Sun Tattauna Hanyoyin Warware Rikicin Zimbabwe Da Congo
Feb 11, 2019 02:12Shugaban kungiyar raya ci gaban kasashen kudancin Afrika (SADC) kana shugaban kasar Namibia Hage Geingob a ranar Lahadi ya gayyaci babban sakataren MDD Antonio Guterres domin tattauna hanyoyin warware dambarwar siyasa a kasashen Zimbabwe da jamhuriyar demokaradiyar Kongo DRC.
-
AU Na Sa Ran Fara Aiki Da Yarjejeniyar Cinikaya A Watan Yuli
Feb 11, 2019 02:02Kungiyar tarayya Afrika, ta bayyana cewa tana sa ran kasashe mambobinta zasu fara aiki da yarjejeniyar cinikaya marar iyaka ta tsakaninsu a watan Yuli na shekaran nan ta 2019.
-
Cutar Ebola Ta Kashe Mutum 500 A Congo
Feb 11, 2019 01:40Bayanai daga Jamhuriya Demokuradiyyar Congo na cewa mutum 500 ne cutar Ebola ta yi ajalinsu a cikin watanni shida a gabashin kasar.
-
Nijar : Bazoum, Ne Dan Takaran Jam'iyya Mai Mulki A Zaben 2021
Feb 11, 2019 00:36Jam'iyyar PNDS-Tarrayya, mai mulki a Jamhuriya Nijar, ta tsaida Mal. Mohammed Bazoum, a matsayin dan takaranta a zaben shugaban kasar na 2021 idan Allah ya kai.