-
Shugaban Kasar Algeriya Zai Nemi Shugabancin Kasar A Karo Na Biyar
Feb 10, 2019 15:50Shugaban kasar Algeriya Abdul'aziz Butaflika zai tsaya takarar neman kujerar shugabancin kasar Algeriya karo na biyar duk tare da rashin lafiay da yake fama da ita.
-
Hukumar Zabe A Najeriya Ta Sake Horar Da Malaman Zabe A Lagos
Feb 10, 2019 15:46Hukumar zabe mai zaman kanta a tarayyar Najeriya ta sake horas da malaman zabe 846 don tabbatar da cewa sun fahinci aikinsu sun kuma gane dukkan abinda ya hau kansu su aikata a ranar zabe.
-
Mayakan Kungiyar Alshabab 30 Ne Suka Halaka A Kasar Somalia.
Feb 10, 2019 15:45Majiyar sojojin kasar Somalia ta bayyana cewa sojojin kasar Sun sami nasarar halaka mayakan kungiyar yan ta'adda ta Al-shabab 30 a yau Lahadi.
-
Sojojin Halifa Haftar A Libya sun Kwace Garin Darne Gaba Daya.
Feb 10, 2019 15:43Majiyar sojojin kasar Libya wadanda suke biyayya ga Janar Halifa Haftar mai ritaya ta bara labarin cewa sojojin kasar sun sami nasara mamaye garin Drne dake gabacin kasar gaba dayansa.
-
Al'Sisi Na Masar Ya Zama Sabon Shugaban Kungiyar AU
Feb 10, 2019 06:31Shugaban kasar Masar, Abdel fatah Al-Sisi, ya karbi shugabancin kungiyar tarayya Afrika na wannan karo a hukumance, daga hannun takwaransa na Ruwanda Paul Kagame.
-
Hadarin Helikoftan MDD, Ya Yi Ajalin Mutum 3 A Sudan Ta Kudu
Feb 10, 2019 06:17Wani hadarin jirgin sama mai saukar ungulu na Majalisar dinkin duniya ya yi sanadiyar mutum uku da kuma raunata wasu 10 a Sudan ta Kudu.
-
Demokradiyyar Congo: An Kashe Fursunoni 12 Da Suke Kokarin Tserewa Daga Kurkuku
Feb 10, 2019 03:45Majiyar gwamnatin kasar ta Demokradiyyar Congo ce ta sanar da mutuwar fursunonin 12 a lokacin da suke kokarin guduwa daga gidan kurkuku na Kasai da ke yankin Tshikapa
-
'Yan Tawaye Sun Rungumi Zaman Lafiya A Nijar
Feb 09, 2019 14:42Wasu 'yan tawaye na kungiyar (MJRN), wanda gwamnati bata amince dasu ba sun sanar da ajiye makaman yaki a yankin Dirkou
-
AFCONU20 : Najeriya Ta Yi Waje Da Nijar Mai Masabkin Baki
Feb 09, 2019 14:00A ci gaba da gasar cin kofin kwallon kafa na Afrika na 'yan kasa da shekara 20, dake gudana a Jamhuriyar Nijar, tawagar kwallon kafa ta Najeriya, ta yi waje da Nijar mai masabkin baki, bayan data doke ta da ci 1-0, a wasan da suka buga jiya Juma'a a Yamai.
-
Sudan Ta Kudu : Kiir, Ya Zargi Kasashen Yamma Da Kawo Cikas Ga Zaman Lafiyar Kasar
Feb 09, 2019 13:19Shugaban kasar Sudan ta kudu Salva Kiir, ya zargi masu bada taimako na kasashen yammacin duniya da gazawa wajen kin samar da kudaden da za'a yi amfani da su wajen aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya wanda zai kawo karshen yakin basasar kasar da aka shafe sama da shekaru biyar anayi a kasar.