-
An Fara Taron AU, Karo Na 32 A Birnin Adis-Ababa
Feb 09, 2019 13:02Yau Asabar, shuwagabannin kasashen Afrika, sun fara taronsu na shekara-shekara, a birnin Adis Ababa, na kasar Habasha
-
Aljeriya : FLN, Ta Tsaida Buteflika A Matsayin Dan Takaranta
Feb 09, 2019 12:29Jam'iyyar FLN, mai mulki a Aljeriya, ta sanar da tsayar da shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika, a matsayin dan takaranta a babban zaben kasar dake tafe.
-
Boko Haram Ta Kashe Sojoji 3 A Najeriya
Feb 09, 2019 12:11Rahotanni daga najeriya na nuni da cewa kungiyar Boko haram ta kashe sojojin kasar a wani hari data kai wani sansanin soji a arewa maso gabashin kasar.
-
Zazzabin Lasa: Yawan Mutanen Da Zazzabin Lassa Ta Kashe A Najeriya Sun Kai 57
Feb 09, 2019 08:21Hukuma mai kula da cututtuka masu haddasa annoba wato "the Nigeria Centre for Disease Contro" ko NCDC ta bada sanarwan cewa yawan mutanen da suka rasa rayukansu sanadiyyar barkewar zazzabin Lassa ya zuwa yanzu ya kai 57.
-
Al'ummar Kasar Sudan Na Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kin Jinin Gwamnati
Feb 09, 2019 01:58A jiya juma'a al'ummar kasar Sudan sun sake gudanar da zanga-zangar kin gwamnati a jihohin daban daban na kasar ciki harda Khartoum babban birnin kasar
-
Saliyo:Za A Aiwatar Da Daurin Rai Da Rai Ga Duk Wanda Aka Kama Da Laifin Fyade
Feb 09, 2019 01:43Shugaban Kasar Saliyo Julius Maada Bio ya bayyana saka dokar ta baci sakamakon cigaba da yawaitar matsalar fyade da cin zarafin kananan yara da ke faruwa a kasar, tare da hukuncin daurin rai da rai a kan duk wanda aka kama da aikata mumunar aika aikar.
-
Kakakin Majalisar Dokokin Ivory -Coast Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa
Feb 08, 2019 15:46Shugaban Majalisar dokokin kasar Ivory-Coast Guilaume Soro ya ajiye aikinsa a yau Jumma'a bayan wani taron gaggawa da ya kira na majalisar dokokin kasar.
-
Kotun Koli A Jihar Rivers Ta Hana Jam'iyyar APC Tsaida Yan Takara A Zaben Gwamna Da Na Yan Majalisun Tarayyar
Feb 08, 2019 15:45Kotun koli a jihar Rivers na tarayyar Najeriya ta yanke hukuncin haramtawa jam'iyyar APC tsaida yan takara a zaben yan majalisar dokokin tarayyar da na gwamna a zabubbuka masu zuwa.
-
Marocco Ya Janye Daga Cikin Kawancen Saudiya Kan Kasar Yemen
Feb 08, 2019 09:25Hukumomin kasar Marocco sun sanar da cewa kasar ta janye daga cikin rundunar kawancen saudiya a kasar yemen tare da kiran jakantanta daga birnin Riyyad.
-
Gobara Ta Cinye Wani Sansanin 'Yan Gudun Hijira A Najeriya
Feb 08, 2019 01:15Rahotanni daga Najeriya na cewa wata mummunar gobara ta cinye wani sansanin 'yan gudun hijira a arewa maso gabashin kasar.