Aljeriya : FLN, Ta Tsaida Buteflika A Matsayin Dan Takaranta
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i35149-aljeriya_fln_ta_tsaida_buteflika_a_matsayin_dan_takaranta
Jam'iyyar FLN, mai mulki a Aljeriya, ta sanar da tsayar da shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika, a matsayin dan takaranta a babban zaben kasar dake tafe.
(last modified 2019-02-09T15:59:59+00:00 )
Feb 09, 2019 15:59 UTC
  • Aljeriya : FLN, Ta Tsaida Buteflika A Matsayin Dan Takaranta

Jam'iyyar FLN, mai mulki a Aljeriya, ta sanar da tsayar da shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika, a matsayin dan takaranta a babban zaben kasar dake tafe.

Jam'iyyar ta bayyana hakan ne birnin Alger a yayin babban gangaminta na gabanin yakin neman zabe.

Dama dai a makon da ya gabata, kawancen Jam'iyyun siyasa guda hudu dake mulki a kasar, sun nuna goyansu a hukumance kan takara shugaban kasar Abdelaziz Bouteflika a zaben mai zuwa.

Wannan shi ne karo na biyar da jam'iyyar ta FLN dake mulkin wannan kasa ta Aljeriya tun bayan samun 'yancin kanta ke tsaida, Abdelaziz Bouteflika, a matsayin dan takaranta a zaben shugaban kasa.

A ranar 18 ga watan Afrilu na wannan shekara ne al'ummar kasar ta Aljeriya ke kada kuri'a a babban zaben kasar, saidai har yanzu shugaban mai shekaru 81, wanda baida cikakar lafiya bai bayyana aniyarsa ba, ta sake tsayawa takara a zaben ba.

A ranar 3 ga watan Maris mai zuwa ne za'a rufe karbar takardun masu sha'awar tsayawa takara a zaben kasar.