Marocco Ya Janye Daga Cikin Kawancen Saudiya Kan Kasar Yemen
Hukumomin kasar Marocco sun sanar da cewa kasar ta janye daga cikin rundunar kawancen saudiya a kasar yemen tare da kiran jakantanta daga birnin Riyyad.
Hukumar Radio da Talabijin ta kasar Iran ta nakalto wani babban jami'in gwamnatin kasar Morocco a jiya alhamis na cewa kasarsa ta janye daga duk wani taron ministoci da kuma bayyar da tallafi a kawancen saudiya dake kai hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar kasar Yemen.
Wannan sanarwa ta gwamnatin Morocco na zuwa ne yayin da ministan harakokin wajen kasar Nasser Bourita ya fada a ranar 24 ga watan janairun da ya gabata, a baya-bayan nan kasar Morocco ba ta halarci atisayi da dama na kawancen saudiya a kasar Yemen ba, kai harda zaman da ministocin kasashen da suke wannan kawance suke yi, kasar ba ta halarta ba.
Tun a wannan Maris din 2015 ne kasar Saudiya bisa cikekken goyon bayan Amurka da hadaddiyar daukar Larabawa da kuma wasu kasashen Larabawa ta fara kai hare-haren wuce gona da iri kan al'ummar kasar Yemen tare da killace kasar ta kasa da kasa da kuma ruwa.
Yayin da yakin ya tunkari shekaru 4, har yanzu kawancen Saudiyar bai cimma manufofinsa ba, face kisan kiyashi kan fararen hula da kuma rusa kasar ta yemen.