Kakakin Majalisar Dokokin Ivory -Coast Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa
Shugaban Majalisar dokokin kasar Ivory-Coast Guilaume Soro ya ajiye aikinsa a yau Jumma'a bayan wani taron gaggawa da ya kira na majalisar dokokin kasar.
Kamfanin dillancin labaran AFP na kasar Faransa ya bayyana cewa, ana daukar Guillaume Soro a matsayin dan takarar shugaban kasa a zaben shekara ta 2020 mai zuwa. Banda haka kasancewarsa tsohon shugaban yan tawaye ne kome na iya faruwa.
Har yanzun dai ba wanda ya ji dalilan da suka sa Guillaume Soro ya ajiye aikinsa ba, amma wasu da dama suna jin tsaron hakan ya jafe kasar cikin rikicin siyasa da kabil;anci.
A shekara 1980 zuwa sama dai kasar Ivory -coast ta yi ta fama da yan tawaye, wanda Guillaume Soro yana daga cikin wadanda suje jagorantar wasu kungiyoyin yan tawayen.
Sai kuma a shekara ta 2010 an fara wani rikici bayan zaben shugaban kasa wanda alhasan watara ya lashe amma shugaban kasa mai ci na lokacin Laurent Gbagbo yaki amincewa ya sauka, da haka kuma aka fara rikicin ya lashe rayukasn muatne fiye da 3000.