Feb 10, 2019 19:15 UTC
  • Mayakan Kungiyar Alshabab 30 Ne Suka Halaka A Kasar Somalia.

Majiyar sojojin kasar Somalia ta bayyana cewa sojojin kasar Sun sami nasarar halaka mayakan kungiyar yan ta'adda ta Al-shabab 30 a yau Lahadi.

Kamfanin dillancin labaran Xinhuwa na kasar Cana ya nakalto majiyar sojojin kasar ta Somaliya tana fadar haka a yau Lahadi. Ta kuma kara da cewa sojojin kasar tare da taimakon na rundunar kasashen Afrika da suke kasar sun sami nasara kashe mayakan alshabab 30 a yankin Juba na birnin Magadishu babban birnin kasar. 

Tun shekara ta 2007 ne mayakan kungiyar Alshaba suke kokarin kifar da gwamnatin tsakiyar kasar Somalia. 

A shekara ta 2011 ne rundunar tabbatar da zaman lafiya na tarayyar Afrika wacce aka girka a kasar ta Somaliya ta sami nasarar korar mayakan na alshaba daga birnin Magadishu babban birnin kasar. Sai dai har yanzun akwai wasu yankuna da dama a kasar ta somalia wadanda mayakan alshabab suke iko da su. 

Tags