Demokradiyyar Congo: An Kashe Fursunoni 12 Da Suke Kokarin Tserewa Daga Kurkuku
Feb 10, 2019 03:45 UTC
Majiyar gwamnatin kasar ta Demokradiyyar Congo ce ta sanar da mutuwar fursunonin 12 a lokacin da suke kokarin guduwa daga gidan kurkuku na Kasai da ke yankin Tshikapa
Majiyar gwamnatin kasar ta Congo sun ce fursunonin sun mutu ne a yayin da jami'an tsaro suke kokarin shawo kansu da hana su tserewa.
Bugu da kari wasu fursunoni 8 sun sami raunuka masu hatsari da ake yi musu magani a asibiti
A gefe daya jami'an tsaron kasar ta Congo biyu sun rasa rayukansu
Majiyar 'yan sanda a yankin na Tshikapa ta ce; Fursunoni 60 sun tsere daga kurkukun amma ya zuwa yanzu an kame 16 daga cikinsu.