An Kawo Karshen Taron Shugabannin Tarayyar Afirka A Kasar Habasha
A jiya Litinin da marece ne aka kawo karshen taron shugabannin kungiyar tarayyar Afirka karo na 32 a birnin Adis Ababa na kasar Habasha
A cikin bayanin bayan taro da shugaban kasar Masar Abdulfattah al-Sisy, da ya karbi shugabancin kungiyar na karba-karba, ya karanta, ya bayyana amincewar shugabannin kasashen kungiyar da gaggauta bude kasuwanci da babu wani tarnaki a cikinsa a tsakanin kasashen nahiyar, da kuma sake gina yankunan da rikice-rikice su ka lalata.
Bugu da kari bayanin taron yana son ganin mutanen da su ka yi hijira saboda fadace-fadace sun koma gidajensu
Har ila yau, shugabannin kungiyar hadin kai Afirkan suna son ganin an yi wa kungiyar kwaskwarima ta yadda za ta yi aiki tukuru domin samar da cigaba mai dorewa da warware matsalolin da nahiyar take fama da su daga tushe
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai aka bude taron shugabannin kasashen nahiyar ta Afirka a birnin Adis Ababa na kasar Habasha