-
Kotun ICC Ta Sallami Tsohon Shugaban Ivory Coast
Jan 15, 2019 11:54Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta sallami tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo, da kuma tsohon ministansa Charles Ble Goude da take tsare da buisa zargin cin zarafin bil adama.
-
Jami'an Tsaro A Kasar Kamaru Sun Kashe Wasu Yan Bindiga A Kasar
Jan 15, 2019 03:51Majiyar jami'an tsaron kasar Kamaru daga garin Bamenda ta bayyana cewa jami'an tsaron kasar sun kashe wasu mutane dauke da makamai su 7 a wani sumamaye da suka kaiwa mabuyarsu.
-
Zanga-zanga Ba Za Ta Kifar Da Ni Ba_El Bashir
Jan 14, 2019 15:56A yayin da yake gabatar da jawabi ga taron magoya bayansa a yankin Darfur, shugaban na kasar Sudan ya ce; Hanya daya ta hawa kan kujerar mulki ita ce akwatunan zabe
-
Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kyammar Gwamnati A Sudan
Jan 14, 2019 08:34Mutanen kasar Sudan suna ci gaba da zanga-zanga a wasu manya -manyann garuruwan kasar wadanda suka hada da Birnin Khartum babban birnin Kasar.
-
An Tsawaita Dokar Ta Baci Da Watanni Uku A Masar
Jan 14, 2019 02:20Majalissar dokokin kasar Masar, ta amince da kara wa'adin dokar ta baci a wasu yankunan kasar da watanni uku.
-
Rashin Tsaro : Buhari Na Najeriya Ya Sake Zargin Gaddafi
Jan 14, 2019 01:26Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya sake zargin tsohon shugaban kasar Libiya, mirigayi Muammar Ghaddafi da zame ummul-aba'isin tabarbarewar al'amuran tsaro a kasashen yammacin Afrika dana tsakiya da dama.
-
Sudan : Jami'an Tsaro Sun Tarwatsa Masu Bore A Khartum Da Darfur
Jan 14, 2019 00:44Jami'an kwantar da tarzoma a Sudan, sunyi amfani da hayaki mai sa hawaye wajen tarwatsa masu zanga zangar kin jinin gwamnati a Khartoum babban birnin kasar da kuma yankin Darfour.
-
Kungiyar (SADC), Ta Bukaci A Sake Kidayar Kuri'un Zabe A D.R Congo
Jan 14, 2019 00:04Kungiyar ci-gaban kasashen kudancin Afirka (SADC), ta bada shawarar a sake kidayar kuri'un zabe a Jamhuriya Demokuradiyyar Congo, domin kwantar da hankali a takaddamar data kunno kai bayan sanar da sakamakon wucin gadi na zaben shugaban kasar.
-
Najeriya: Wata Babbar Mota Ta Kashe Mutune 20 A Jihar Ekiti
Jan 13, 2019 15:37Majiyar Jami'an tsaro a tarayyar Najeriya ta bayyana cewa mutane akalla 20 ne suka rasa rayukansi a lokacinda wata mota babban ta burma a cikin wata kasuwa a jihar Ekiti daga kudancin kasar a jiya Asabar.
-
Ofishin Jakadancin Najeriya A Habasha Ta Bukaci Yan Najeriya Su Bayyana Kudade Wadanda Suka fi $3000 Ga Jami'an Tsaron Kasar
Jan 13, 2019 15:35Ofishin jakadancin tarayyar Najeriya a birnin Adis Ababa na kasar Ethiopia ya bukaci dukkan yan Nigeriya masu zuwa kasar su nunawa jami'an Costam na kasar kudade wadanda suke fi dalar Amurka 3000 da kuma golagolai da suke tare da su.