Jan 14, 2019 19:26 UTC
  • Zanga-zanga Ba Za Ta Kifar Da Ni Ba_El Bashir

A yayin da yake gabatar da jawabi ga taron magoya bayansa a yankin Darfur, shugaban na kasar Sudan ya ce; Hanya daya ta hawa kan kujerar mulki ita ce akwatunan zabe

Shugaban na kasar Sudan ya kara da cewa; A lokacin zaben da za a gabatar a 2020 ne al'ummar kasar ta Sudan za su yanke hukunci akan wanda zai jagoranci kasarsu

Umar Hassan al-Bashir ya jaddada cewa; Ba za mu bari wani mahaluki ya hargitsa kasarmu ba ko kuma ya lalata dukiyar al'umma."

Tun a ranar 19 ga watan Disamba na 2018 ne al'ummar Sudan su ka fara gudanar da Zanga-zangar kin amincewa da hauhawar farashin kayan masarufi wacce ta juye zuwa yin kira ga shugaban kasar da ya sauka daga kan mukaminsa

Wani kwamitin bincike na gwamnati ya bayyana cewa; Adadin wadanda su ka rasa rayukansu a sanadiyyar tashe-tashen hankula masu alaka da Zanga-zangar sun kai24, sai dai majiyar kungiyoyin kare hakkin bil'adama na cikin gida da waje, sun ce mutane 40 ne jami'an tsaro su ka kashe.

 

Tags