Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kyammar Gwamnati A Sudan
https://parstoday.ir/ha/news/africa-i34801-ana_ci_gaba_da_zanga_zangar_kyammar_gwamnati_a_sudan
Mutanen kasar Sudan suna ci gaba da zanga-zanga a wasu manya -manyann garuruwan kasar wadanda suka hada da Birnin Khartum babban birnin Kasar.
(last modified 2019-04-27T09:55:10+00:00 )
Jan 14, 2019 08:34 UTC
  • Ana Ci Gaba Da Zanga-Zangar Kyammar Gwamnati A Sudan

Mutanen kasar Sudan suna ci gaba da zanga-zanga a wasu manya -manyann garuruwan kasar wadanda suka hada da Birnin Khartum babban birnin Kasar.

Kamfanin dillancin labaran Anatoliyo ya bayyana cewa a jiya Lahadi ma an gudanar da zanga-zanga a khartum babban birnin kasar da kuma garuruwan Al-Fashir, Al-Fai da kusa da birnin Port Sudan na bakin ruwa. 

Labarin ya kara da cewa a birnin Port Sudan jami'an tsaro sun yi amfani da hayaki masu sa hawaye don tarwatsa masu zanga-zanga. 

A dai-dai wannan lokacin ne jam'iyya mai mulkin kasar ta bayyana cewa idan har masu zanga zanga basu daina fifotuwa gwamnatu zata dauki matakin da yafi wanda suke dauka a halin yanzu.

Sai dai gamayyar jam'iyyun siyasar kasar da wasu kungiyoyi masu zanga kansu sun  bada sa sanarwan cewa zasu fito gagarumin zanga-zanga a ranar Alhamis mai zuwa.