Rashin Tsaro : Buhari Na Najeriya Ya Sake Zargin Gaddafi
(last modified Mon, 14 Jan 2019 04:56:30 GMT )
Jan 14, 2019 04:56 UTC
  • Rashin Tsaro : Buhari Na Najeriya Ya Sake Zargin Gaddafi

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya, ya sake zargin tsohon shugaban kasar Libiya, mirigayi Muammar Ghaddafi da zame ummul-aba'isin tabarbarewar al'amuran tsaro a kasashen yammacin Afrika dana tsakiya da dama.

A cewar Buhari, wanda kasarsa ke sahun gaba wajen fama da matsalar Boko Haram, duk da cewa mutuwar Gaddafi ta rura lamarin, amma tun kafin hakan, Gaddafi, ya baiwa matasan Afrika ta yamma da dama horo da kuma makaman yaki, wadanda kuma su ne a yau sune suke cikin kungiyoyi masu dauke da makamai a yankin. 

Buhari, wanda ke bayyana hakan a wata hita da gidan talabijin na ''Arise TV'' da aka watsa a makon da ya wuce, ya kara da cewa 'yan tada kayar baya da suka arce daga Libiya bayan mutuwar Gaddafi a cikin shekara 2011, sun koma aikata ayyukan ta'addanci a wasu kasashen yankin ciki har da Najeriya, duba da matsalar Boko haram da kuma fulani masu dauke da makamai.

Shugaba Buhari ya kara da cewa, Gaddafi wanda ya shugabanci Libiya na tsawan shekaru 43, a wani lokaci ya dauki mutane 'yan asalin kasashen Mali, Burkina Faso, Nijar, Najeriya da Chadi da Jamhuriya Afrika ta tsakiya, maimakon ya basu horo akan ayyukan gine-gine, ko gyaren wuta da dai saurensu, kawai sai ya koya masu ''harbi da kisa'', wanda kuma yau wadanda suka tsere daga kasar bayan faduwar gwamnatinsa ke kai hare hare a arewa maso gabashin Najeriya, da wasu kasashen yankin.

Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da Shugaba Buhari yake firta irin wadannan kallaman, wadanda yake ganin su ne silan rashin murkushe kungiyar boko haram dake ci gaba da kai hare hare a wasu sassan arewacin kasar ta Najeriya.

Wasu masana dai na ganin akwai kanshin gaskia a cikin bayyanan na Buhari, duba da yadda muggan makaman yaki suka bazu a yankin.