Kotun ICC Ta Sallami Tsohon Shugaban Ivory Coast
Kotun hukunta manyan laifuka ta duniya ta sallami tsohon shugaban kasar Ivory Coast Laurent Gbagbo, da kuma tsohon ministansa Charles Ble Goude da take tsare da buisa zargin cin zarafin bil adama.
Wannan matakin ya biyo bayan da alkalan kotun ta ICC ko kuma CPI, suka zartar da hukuncin cewa basu da laifi, duba da yadda masu shigar da kara suka gaza bayar da gamsasshiyar shaida kan tuhume-tuhumen da ake wa tsaffin jami'an biyu ba, a don haka alkalan suka bada umarnin a sake su ba tare da wata-wata ba.
M. Laurent Gbagbo, wanda shi ne wani tsohon shugaban kasa na farko da aka gurfanar a gaban kotun ta ICC, ana zarginsa da laifukan cin zarafin bin adama a rikicin da ya biyo bayan zaben kasar a tsakanin 2010 zuwa 2011, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu uku a cikin watannin biyar.
Tsohon shugaban kasar ta Ivory Coast, ya kwashe shekaru bakai a gidan kason kotun ta ICC dake birnin Hague.
Tuni dai 'yan uwa da magoya bayan tsohon shugaban kasar suka fantsama kan tituna domin nuna murnarsu dangane da matakin kotun.
A cikin shekara 2011 ne dakarun Faransa dana MDD, wadanda ke goyon bayan abokin hamayyarsa Alassane Ouattara, suka kama M. Gbagbo a wata maboyar karkashin kasa da ke fadar shugaban kasar.